Kwamitin sasantawa tsakanin manoma da makiyaya ya sami nassara a Zuru

A bisa kokarin ganin an sami wanzuwar zaman lafiya tare da wadatar kwaanciyar hankali a kasar Zuru musamman tsakanin Manoma da Makiyaya al'ummar Fulani ,shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru Alh. Muhammed Kabir Abubakar ya nada wani Kwamiti mai karfi sakamakon murubar mutane da aka saka a cikin Kwamitin wacce ta duba tare da sake tanadi akan Burtulla da Mashaya a kasar Zuru.

Sakamakon wannan namijin kokari da hangen nesa a tsari na fahimtar samar da zaman lafiya , ya bayyana a zahiri yadda shirin ya samu nassara ganin yadda Kwamitin ya sami nassara wajen tafiyar da aikinsa bisa irin goyon baya da Manoma tare da Makiyaya da lamarin ya shafa suka bashi a lokacin gudanar da aikinsa wanda hakan ya mayar da zaman lafiya da fahimta tsakanin bangarorin biyu.

Shugaban Kwamitin sasantawa tsakanin Manoma da Makiyara ya shaida mana cewa Kwamitin ya duba yanayi na Burtula na kasa da kasa, na jiha da kuma na karamar hukuma, gunduma shida ne Kwamitin ya ziyarta a Masarautar Zuru.

Kwamitin ya hada da Ayuba Dogo tsohon daraktan tsare-tsare SUBEB wanda shi ne shugaban Kwamitin tare da Sakataren Kwamitin  Dr. Gondi Gonta da sauran manbobi kamar Aminu Muhammed Sakaba daga sashen inganka lafiyar dabbobi na Makarantar gona ta jiha da ke garin Zuru.

Ya kuma kara da cewa a wasu wurare da Kwamitin ya gudanar da aiki ya ta lura cewa Manoman ne ke da shanaye kuma suna bukatar a fitar da Burtula. Haka zalika Kwamitin ya yaba akan goyon baya da bangarorin biyu suka bayar musamman wajen fitar da Mashaya, Burtali da Mashekari.

Shugaban Kwamitin ya bukaci shugaban karamar hukumar Zuru ya kara masu lokaci domin gundumar Dabai da Senchi suna da girma sosai ganin cewa sakamakon harkar rayuwa tsakanin Manoma da Makiyaya wasu Burtula da Mashaya an shafe su gaba daya wanda yace haka ya zama wajibi a natsu wajen sake tsarawa tare da fitar da su.

Isyaku Garba daga Zuru

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN