Jihar Kebbi: Ko wajibi ne ka kasance dan wata kungiya ?

Kungiya wani tsari ne da mutane ke kafawa bisa wata manufa domin samun biyan bukata bisa wani abu da ake so ko ake nufi kuma wanda ba za a iya samun nassara akan lamarin ba sai mutane da suke da manufa da fahimta daya kan lamarin sun hada kansu a waje daya kuma su sami izini ko yardar hukuma domin su dinga gudanar da lamarinsu tare da sanin hukuma.

Bisa wannan maudu'in, kasancewa cikin kungiya ko rashin kasancewa a cikinta ya danganci irin manufa da tsari hadi da nagartar mutuncin wadanda ke tafiyar da kungiyar.

A bangaren hukuma ko doka, bincike ya nuna cewa kowane dan Najeriya yana da yancin kasancewa dan kungiya da yake so haka zalika babu tilas akan cewa dole sai ya zama dan wata kungiya.

Sabanin yadda wasu jami'an tsaro suka yi ta yi wa wadansu masu gyaran wayar salula a cikin garin Birnin kebbi barazana cewa ala tilas sai sun kasance yan wata kungiya ta zalunci, rashin amana,cin zarafi da kuma akida wanda aka gina ta hanyar jayayya da hukuncin Allah.

Ita wannan kungiya tana ikirarin cewa masu gayaran wayar salula da masu sayar da wayar salula duka daya ne. Amma gaskiyar lamari shine zancen ba haka yake ba, domin a harkar sayar da wayar salula baka bukatar horo domin ka fara sayar da waya. Amma a wajen gyaran wayar salula dole sai an koyar da kai yadda za ka gyara wayar salula kafin ka fara gyara.

Misali anan shine idan ka kalli yadda masu harkar mota ke tafiyar da harkokinsu cikin tsari, domin sun samar da ka'ida da daidaito bisa kwarewar mutum a kan sana'ar mota, ka gan akwai kungiyar masu sayar da mota zalla, akwai kungiyar masu jigila na fasinja watau NURTW akwai kuma kungiyar kanikawan mota watau NATA kuma kowace kungiya tana cin gashin kanta ne bisa tsari na ilimi.

Saboda haka mai gyaran wayar salula a jihar Kebbi yana da tashi kungiya wacce ba ta da alaka da mai sayar da wayar salula kuma sunanta shine MOBILE PHONE YOUTH ELITE TECHNICIANS OF KEBBI STATE (ELTECH) kuma ba tilas a harkar shiga kungiyar ELTECH. Amma yana da kyau duk mai gyaran wayar salula matukar yana gyara HARDWARE ko SOFTWARE yana da yancin ya zama dan kungiyar ELTECH na jihar Kebbi.

Daga Isyaku Garba

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN