Kalli dubban mutane da suka halaci jana'izar Jaruma Sridevi - Hotuna

Dubban mutane ne suka bayyana yau a titunan birnin Mumbai yayin da aka fito da gawar Jarumar Finafinan Bollywood na kasar India Sridevi Kapoor a wani jerin gwanon motoci da suka yi wa gawar rakiya.

A shekara ta 1980s lokacin da tauraruwar Jarumar ke tsananin haskawa, Sridevi ta kasance Jaruma wacce ta fi sauran Jarumai Mata yawan albashi.

Sridevi ta rasa ranta ne sakamakon wani hadarin cikin gida bayan ta darje a cikin bahon wanka da ke bandaki a wani Hotel a hadaddiyar Daular Larabawa UAE mako da ya gabata.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Kalli dubban mutane da suka halaci jana'izar Jaruma Sridevi - Hotuna Kalli dubban mutane da suka halaci jana'izar Jaruma Sridevi - Hotuna Reviewed by on March 02, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.