Ka san abin da boko haram ta bukata kafin ta sako yan matan Dapchi ?

Shugaban hukumar DSS na Najeriya Lawal Musa Daura ya ce kungiyar boko haram ta bukaci a tsagaita buda wuta da sojin Najeriya ke yi masu babu kakkautawa, kuma a bisa wannan shiri kungiyar ta sako yan matan makarantar Dapchi da ta sace kimanin wata daya da ya gabata.

Lawal Daura ya shaida haka ne yayin da yake gabatar da yan matan ga shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Aso da ke Abuja.

Idan baku manta ba, shugaban kungiyar ta boko haram ya yi Allah wadai kan irin yadda sojin Najeriya suka addabi yan kungiyar da hare-hare da wasu kafofin watsa labarai suka ambato shugaban na boko haram Abubakar shikau ya kira "bala'i daga sojin Najeriya".

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Ka san abin da boko haram ta bukata kafin ta sako yan matan Dapchi ? Ka san abin da boko haram ta bukata kafin ta sako yan matan Dapchi ? Reviewed by on March 25, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.