Dan acaba ya yi yunkurin kashe kanshi domin hukuma ta kwace masa babur

Yansanda sun kama wani matashi mai suna Hammed Tijjani  wanda ya yi yunkurin kashe kanshi bayan yan sanda sun kama bubur da yake tukawa a birrnin Lagos.Lamarin ya faru a kofar shiga caji ofis na Isolo bayan Tijjano ya ruga da gudu kuma ya kwanta a kasar babbar mota da ta ke dauke da baburra ciki har da nashi zuwa Oshodi.

Bayanai sun nuna cewa matukar aka kai babur zuwa Oshodi lallai wannan babur an yi assarar sa kenan har abada bisa sabuwar dokar jihar Lagos

An gurfanar da Tijjani a gaban wata Kotun Magistare amma Alkalin Kotun Mrs. O.A Teluwo ta bayar da bilinsa har zuwa zaman Kotun na gaba yayin da aka tasa keyarsa zuwa Kurkuku kafin ya cika ka'idodin beli.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Dan acaba ya yi yunkurin kashe kanshi domin hukuma ta kwace masa babur Dan acaba ya yi yunkurin kashe kanshi domin hukuma ta kwace masa babur Reviewed by on March 19, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.