B-kebbi: Lalata da yarinya yar shekara 9 a Badariya, Kotu ta ki bayar da beli

Wata kotun Majistare ta 1 da ke Birnin kebbi ta ci gaba da sauraron shari'ar wani dan kabilar Igbo wanda aka gurfanar a gabanta mako da ya gabata bisa zargin yin lalata da yarinya yar shekara 9 a unguwar Badariya.

Mai shari'a Justice Kakale Mungadi ya saurari bayanan ita yarinyar a asirce cikin Ofishinsa saboda kariya ga yarinyar daga yiwuwar fallasa bayan mai gabatar da kara na yansanda ya roki Kotu ta duba yanayin yarinyar da shekarunta, yayin da aka ci gaba da sauraron shari'ar a cikin dakin Kotu.

Bayan shaida na farko ya yi wa Kotu bayani kan abin da ya gani a ranar da lamarin ya faru, Alkalin Kotun Justice Kakale Mungadi ya dage zaman Kotun har zuwa ranar 9 ga watan Aprilu domin ci gaba da shari'ar.

Lauyan wanda aka yi kara ya bukaci Kotu ta bayar da belin wanda aka yi kara, amma Alkalin Kotun bai aminta da bukatar ba ya kuma ce Lauyan sai dai a gabatar da bukatar haka a rubuce bisa ka'ida. Daga bisani Alkalin Kotun ya yi umarni a tasa keyar wanda ake zargi zuwa Kurkuku har zuwa ranar 9 ga watan Aprilu 2018 domin ci gaba da shari'ar.

Daga Isyaku Garba

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
B-kebbi: Lalata da yarinya yar shekara 9 a Badariya, Kotu ta ki bayar da beli B-kebbi: Lalata da yarinya yar shekara 9 a Badariya, Kotu ta ki bayar da beli Reviewed by on March 29, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.