An kashe direba da ya yi smogal na shinkafa zuwa Najeriya a Sokoto

Wani rahotu da ya fito daga jihar Sokoto ya nuna cewa jami'an tsaro sun harbe wani direban mota wanda ya fito daga Jamhuriyar Niger makare da buhuhuwan shinkafa a cikin motarsa kuma ya ke kokarin shigowa da su Najeriya.

Rahoton ya ce takaddama ta taso ne bayan jami'an tsaron sun bukaci direban motar ya biyo su su je ofishinsu ganin cewa buhuhuwan shinkafa da ke cikin motar shinkafar kasar waje ce, amma sai direban ya ce sam shi ba zai bi su zuwa ofis ba.

Sakamakon haka zafafar muhawwara ya kaure a tsakanin jami'an tsaron da direban wanda ya kai ga harbi.Wata majiya ta ce bayan an harbe direban a kai wanda ya yi sanadin mutuwarsa nan take sai jami'an suka kwashe tarkacen su suka tafi.

Babu wani bayani daga hukumomin tsaro a Sokoto dangane da wannan lamari kawo yanzu.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
An kashe direba da ya yi smogal na shinkafa zuwa Najeriya a Sokoto An kashe direba da ya yi smogal na shinkafa zuwa Najeriya a Sokoto Reviewed by on March 05, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.