A karshen mako da ya gabata watau ranar Asabar 24 ga watan Febrairu Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya ziyarci mazabarsa ta Zuru.Daga bisani ya halarci daurin Auren Aina'u Abdullahi wacce aka aurar da ita ga Umar Sani a kan Sadaki N50.000.Mataimakin Gwamna Samaila Yombe ne Uban Amarya a wajen addu'ar daurin auren bisa wakilcin karramawa kuma shi ne ya bayar da auren Aina'u ga Umar.
Addu'ar daurin auren ya sami halarcin daruruwan jama'a daga yankin Zuru da kewaye har da wadanda suka zo daga wajen jihar Kebbi.Imam Hassan na Masallacin Juma'a na Izala1 ne ya daura auren ya kuma roki Allah ya albarkaci auren.Manyan Limamai da Ulama sun sami halartar addu'ar daurin auren.
Haka zalika Manyan Mutane daga kowane fanne na rayuwa sun sami halaratar wannan auddu'ar daurin aure wanda ya hada da Sakataren jam'iyar APC na jihar Kebbi Alh. Abubakar Kana, Dan Majalisa mai wakiltar Zuru Hon. Sani Ka'ida, shugaban karamar hukumar Zuru Alh. Muhammad Kabir Abubakar, shugaban hukumar zabe na jihar Kebbi Alh. Kabiru Yakaji, Alh. Jafaru (clean),Alh.Muhammad Ankwai, Alh. Isah Abdullahi Zuru da sauransu.
Bayan haka ,Yombe ya halarci taron wa'azi na kasa da kungiyar Izala ta shirya a garin Ribah tare da tawagarsa .
Daga Isyaku Garba
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com