Yawan jima'i ya sa mata ta kai karan miji Kotu domin a raba aure

A birnin Lagos wata mata ce mai suna Adenike Bolarinwa ta kai karan mijinta  kara a wata Kotu da ke unguwar Agege tana neman Kotun ta raba aurenta da mijinta bisa zargin cewa ita ta gaji da zukun jima'a ba kakkautawa tare da cin mutunci da muzgunawa da mijinta ke yi mata.

Madam Adenike ta shaida wa Kotu cewa maigidanta mutum ne mara mutunci, kuma mai yawan dukanta bayan kafewa da yake yi wajen jima'i lamari da ta ce ba za ta ci gaba da jurewa ba.

Amma maigidanta  ya musanta haka , kuma shi cewa ya yi ma matarsa mace ce da ba ta da mutunci balle ragowa ya kuma shaida wa Kotu cewa shi kam yana son matarsa kuma kada Kotu ta raba aurensu.

Alkalin Kotun Mrs Ibironke Elabor ta bukaci ma'auratan su zauna lafiya tare da kaurace wa tashin hankali har zuuwa lokaci da Kotu za ta dauki mataki da ya dace. Daga bisani Alkalin ta dage shari'ar har zuwa 1 ga watan Maris.
 Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Yawan jima'i ya sa mata ta kai karan miji Kotu domin a raba aure Yawan jima'i ya sa mata ta kai karan miji Kotu domin a raba aure Reviewed by on February 11, 2018 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.