• Labaran yau

  February 15, 2018

  Rashin biyan kudi ya sa asibiti yin garkuwa da jaririya har tsawon wata 5

  Wani Asibiti a gabacin kasar Gabon ya tsare wata jaririya har tsawon wata biyar sakamakon gazawar mahaifiyarta wajen biyan kudin Asibiti wanda ya kai CFA miliyan 2 watau dala 3.630.

  Mahaifiyar jaririyar Sonia Okome ta kasance cikin farinciki bayan jama'a sun tara kudi suka biya bashin Asibitin mai zaman kansa daga bisani aka ba ta jaririyarta.

  Bayanai sun nuna cewa zancen ya kai ga kunnen shugaban kasar ta Gabon Ali Bongo wanda shi ma ya bayar da nasa taimako.

  Wata majiya ta labarta cewa hukumomi a kasar ta Gabon sun kama babban Likita na Asibitin bisa zargin sace jariri amma daga bisani aka yi watsi da wannan tuhumar.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Rashin biyan kudi ya sa asibiti yin garkuwa da jaririya har tsawon wata 5 Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama