Kalli wasu ayyuka da shugaban karamar hukumar Zuru ya yi - Hotuna

Bisa umarnin Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu kan shugabannin kananan hukumomi cewa su tabbata cewa sun yi wa jama'arsu aiki tukuru, shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru Alh. Muhammed Kabir Abubakar ya kammala gyare-gyaren wasu Motoci masu amfani ga jama'a.

Cikin motocin da shugaban karamar hukumar ya gyara sun hada da Katapila Changhin PY190H , Motar kashe gobara kirar Marsandi 1113,Bus na aikin yau da kullum kirar Volkswagen da kuma motar daukan marasa lafiya kirar Toyota mai jiniya .

Shugaban karamar hukumar zuru karkashin jagorancin Hon. Alh Muhammed Kabir Abubakar har ila yau ya gina wasu rijiyoyin burtsatse domin amfanin jama'ar kasar Zuru.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Kalli wasu ayyuka da shugaban karamar hukumar Zuru ya yi - Hotuna Kalli wasu ayyuka da shugaban karamar hukumar Zuru ya yi - Hotuna Reviewed by on February 15, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.