• Labaran yau

  February 27, 2018

  Kalli barawon babur da irin mabudi da yake amfani da shi - Hotuna

  An kama wani matashi mai suna Chinonso Azubuike bayan ya yi yunkurin satar wani babur a Mahautar Musa da ke garin Agbor . Chinonso dai dan asalin garin Onitsha ne kuma ya ce ya je Agbor ne domin ya saci. babur.

  Barawon ya shaida wa yan kungiyar da suka kama shi wanda kungiyar banga ce da ke samar da tsaro a wannan yankin cewa akwai wanda yake jiran a kawo masa baburan sata shi kuma zai saye nan take ya basu kudi a garin Onitsha.

  Daga bisani an mika barawon ga yansanda domin bincike da gurfanarwa a gaban Kotu.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kalli barawon babur da irin mabudi da yake amfani da shi - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama