Gwamna Bagudu zai bayar da bashin N400m ga kungiyar direbobin jihar Kebbi

Daga Isyaku Garba - Birnin kebbi |

Shugaban kungiyar direbobi na kasa NURTW Alh.Dr. Najeeb Usman Yasin (Makaman Gusau) ya ce shugaba Muhammadu Buhari ne mafi dacewa da ci gaba da shugabancin Najeriya a karo na biyu.Alh.Muhammadu ya shaida haka ne a yayin da yake jawabi a lokacin wani taron gangami da kungiyar NURTW ta kasa ta shirya domin nuna goyon baya ga shugabancin Najeriya ,jihohi da kananan hukumomi da jam'iyar APC ke yi.

Shugaban wanda Auditan kungiyar ta kasa Alh. Yahuza 'Yankaba ya wakilta ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da kwarjini tare da kwarin guiwa ga direbobi sakamakon inganta tsaro da Gwamnati ta yi a hanyoyin mota a fadin kasarnan.

Ya kuma nuna goyon baya akan mataki da reshen kungiyar ta jihar Kebbi ta dauka na nuna goyon bayan ta na amincewa da shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Atiku Abubakar Bagudu su sake tsayawa takara a 2019.

Haka zalika shugaban kungiyar reshen jihar Kebbi Alh.Usman Abubakar Bagudu ya umarci dukannin mambobin kungiyar su zabi shugaba Buhari da Gwamna Bagudu a karo na biyu. Ya ce hakan ya biyo bayan irin nassarori kan harkar ci gaba da ya bayyana a tsarin shugabancinsu.


Yayan Gwamna Bagudu watau tsohon 'dan Majalisar wakilai Alh.Bello Bagudu (Wakilin Gwandu) shi ne ya karbi takardar bukatar ya mika wa Gwamna Atiku Bagudu domin isarwa ga shugaba Muhammadu Buhari.

A nashi jawabi, Gwamna Atiku Bagudu ya gode wa kungiyar ta direbobi saboda yadda ta bayar da gagarumin gudunmowa wajen tabbatar da kafa Gwamanatinsa ta hanyar zabensa.

Gwamana Bagudu ya ce Gwamnatinsa za ta bayar da rancen Naira Miliyan dari biyu ga kungiyar ta direbobi domin su saye motoci da zai taimaka wajen bunkasa sana'ar su, haka zalika za' a samar da bashin Naira Miliyan dari biyu ga kungiyar (NARTO) domin inganta sana'arsu.




Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN