Ba dubun dubatan Dakkarawa ne suka karbi Kwankwasiyya ba - Alh.Musa Zuru

Sakamakon wani rubutu da wani mai suna Sabi'u Labbo Yandu Kamba ya rubuta a shafin sada zumunta wanda ya haifar da cece-kuce daga wasu mutane a Masarautar Zuru da lamarin ya shafa inda shi wanda ya yi rubutun ya nuna cewa dubu dubatan mutane a kasar Zuru sun tarbe 'yan kungiyar Kwankwasiyya da suka je kasar ta Zuru ranar 10/2/2018 yawan mutane da suka je wajen wannan taron ba gaskiya bane .

Majiyar mu ta tabbata mana cewa adadin mutanen da suka halarci wannan taron na masu da'awar Kwankwasiyya a kasar Zuru basu wauce mutum 150 ba kuma an bamu hujjoji da suka shafi faifan bidiyo da yake dauke da ilahirin yawan mutanen da suka je wannan taron.

Bugu da kari binciken mu ya tabbatar da cewa taron bai sami halarcin Mai Martaba Sarkin Zuru ba haka zalika babu wakilci ko kasancewar daya daga cikin 'yan Majalisarsa.

Bayan haka babu wani fitaccen jigo a harkar siyasar kasar Zuru da kewaye da ya halarci wannan taron a ranar Asabar 10 ga watan Febrairu.

Binciken mu ya nuna mana cewa har ila yau babu kanshin gaskiya a kan bayanin mai rubutun cewa Dakkarawa sun bi Kwankwasiyya a ranar wannan taron.Binciken mu ya kuma nuna cewa babu mutum daya da aka karbe shi kasancewa sabon shiga tafiyar ta Kwankwasiyya a kasar Zuru a wannan ranar.

Wani bawan Allah mai suna Alh. Musa Zuru mazauni unguwar Zango ne a garin Zuru ya shaida mana cewa, "Ni dai abin da na fahimta shine wasu yara ne kawai suke son su burge uwayen gidansu cewa suna gudanar da aiki, amma zahiri babu wani babban mutum da ya halarci wannan taron, kuma ai kowa ya ga yawan mutanen da suka halarci taron. Gaskiya taronnan bai muce mutum 150 idan ma sun kai".

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN