An kashe wanda ya yi sojan gona ya yi fashi a gidan wata mata

An kashe daya daga cikin wasu mutane da suka yi sojan gona wai su jami'an PHCN ne kuma suka sami shiga gidan wata mata a unguwar Sharada da ke cikin birnin Kano, daga bisani kuma suka yi mata fashi suka kwace na'urar komputa da wayoyin salula da sauran kayaki.

Daga bisani mutanen sun fita suka tsere, ganin haka ya sa matar ta fito ta yi ta kururuwar neman taimako lamari da ya sa wasu matasa suka bi su da gudu suka kama daya daga cikin su kuma ya sha duka har ya mutu. Su kuma sauran sun arce.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
An kashe wanda ya yi sojan gona ya yi fashi a gidan wata mata An kashe wanda ya yi sojan gona ya yi fashi a gidan wata mata Reviewed by on February 23, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.