Rundunar 'yansanda a jihar Niger ta kama wasu sojan bogi guda biyu sanye da tufafin soja bayan sun yi wa wani sojin gaske Sgt. Usman Saidu fashi wanda ke aiki da rundunar tsaron lafiyar fadar shugaban kasa Asokoro a cikin Abuja.
Wata majiya ta cewa wadanda aka kama sun dade suna addabar mazauna unguwar Dutsen Zuma da Madalla na yankin Suleja a jihar Niger.
Wadanda aka kama su ne Peter Ali dan shekara 27 da Paul Isyaku dan shekara 23, an kama samarin guda biyu ne bayan sun yi wa sojan fashin motarsa kirar Honda Accord yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Abuja daga bisani matasan suka karbe masa motar da sauran ababen da ke ciki.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Tags:
LABARI