An kama mutum 18 sakamakon rikicin kasuwar magani a Kaduna

Hukumomin tsaro a jihar Kaduna sun kama mutum 18 sakamakon tashin hankali da ya yi sanadin mutuwar wasu mutane a Kasuwan Magani na karamar hukumar Kajuru  a jihar Kaduna ranar Litinin.

Wannan ya biyo bayan ziyarar gani da ido ne a Kasuwar Magani da manyan jami'an tsaro na jihar Kaduna suka yi karkashin jagorancin GOC Rundunar soji ta 1, Kwamishinan yansanda da Daraktan hukumar SSS na jihar Kaduna ranar Talata.

Tawagar ta duba yawan asara da barna da aka yi a Kasuwar tare da tantance bayanai bayan sun zanta da jama'a mazauna wurin tare da jami'an tsaro da aka tura domin kwantar da rikicin.

Daga karshe GOC  na runduna ta 1 ya bukaci a kai zukata nesa kuma a kauce wa aniyar ramuwar gayya tare da kira ga Sarakunan yankin, Malaman addini da shugabannin al'umma su mayar da hankali wajen isar da sakon zaman lafiya ga al'ummarsu.

Manyan jami'an tsaro da suka kai ziyarar sun hada da Major General Mohammed Mohammed GOC Rundunar soji ta 1, Kwamishinan yansanda Austin Iwar, Darakta SSS na jihar Kaduna Mohammed Wakil, Kwamanda na NSCDC AM Bunu, Mai ba gwamna shawara kan harkar tsaro Col. Yakubu Yusuf (murabus) da Samuel Aruwan, Mai ba gwamna shawara kan harkar sadarwa.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN