Zakzaky ya ce ya samu shanyewar barin jiki

Shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka fi sani da 'yan Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya ce ya yi fama da karamin shanyewar jiki a cikin makon jiya.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a karon farko ranar Asabar tun bayan da aka kama shi fiye da shekara biyu da suka wuce.

Malamin addinin ya bayyana ne a Abuja tare da maidakinsa Zeenah wadda ake tsare da su tare.

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ce ta kama Sheikh El-Zakzaky a watan Disambar shekarar 2015 a

Zaria da ke jihar Kaduna, bayan sojoji sun yi wa gidansa kawanya.

Wata sanarwa da kafar watsa labarai ta PR Nigeria fitar na dauke da hotunan Malamin a lokacin da yake jawabi ga 'yan jaridar.

Gidan talbijin na Channels ya ambato Sheikh El-Zakzaky na cewa yana nan a raye kuma lafiyarsa lau.

Ya kuma gode wa 'yan Najeriya saboda addu'o'in da suke yi masa.

A makon nan ne dai aka yi jitar-jitar cewa malamin ya rasu.

Ga yadda ganawarsa ta kasance da 'yan jarida:

'Yan jarida: Barka da rana?

'Yan jarida: Ko za ka iya ganawa da mu?

Sheikh El-Zakzaky: Idan sun amince kuma sun ba ni izini (kamar yadda ya ce cikin raha)
Sheikh Zakzaky: Wane hali kake ciki?

'Sheikh Zakzaky: Na samu shanyewar barin jiki a ranar Juma'a 5 ga watan Janairun bana

Sheikh Zakzaky: Jikin ya yi tsanani ranar Litinin, amma daga baya jikin ya yi sauki

'Yan jarida: Yaya kake ji yanzu haka?

Sheik El-Zakzaky: Ina samun sauki jami'an tsaro sun bari na gana da likitan. Ina godiya ga Allah. Ina samun sauki. 

'Yan jarida: Kana da wani abu da za ka kara cewa.

Sheikh El-Zakzaky: Ina godiya ga addu'o'inku.

'Yan jarida: Mun gode

Sheikh El-Zakzaky: Na gode.

Zakzaky ya shafe fiye da shekara biyu a hannun gwamnatin Najeriya

Sau da dama kotunan kasar suna bayar da umarni ga gwamnatin Najeriya ta saki Malamin, sai dai ba ta yi hakan ba.

Mabiya Malamin sun gudanar da jerin zanga-zanga da zummar matsa lamba ga gwamnatin ta sake shi.

Sun yi zargin cewa ana tsare da shi ba bisa ka'ida ba, ko da yake ministan shari'ar kasar Abubakar Malami ya shaida wa BBC kwanakin baya cewa suna ci gaba da tsare shi ne saboda sun daukaka kara a kan umarnin da kotunan suka bayar.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Daga BBCHausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN