Tunawa da tsoffin soji a jihar Kebbi, Yombe ya bukaci sadaukar da kai

Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya jagoranci bikin tunawa da tsofaffin soji ranar Litinin a filin wasa na Haliru Abdu da ke garin Birnin kebbi babban birnin jihar Kebbi inda aka gudanar da pareti tare da harba harsashi 21 daga bindigogin soji wadanda suka yi shiga ta kawa bayan Gwamna da manyan baki sun saka hure don tunawa da soji da suka rasa rayukansu domin tabbatar da tsaron Najeriya.

Gwamna Bagudu tare da mataimakinsa Col. Samaila Yombe Dabai Mai murabus,Kwamishinan 'yansanda na jihar Kebbi, Wakilin Mai martaba Sarkin Gwandu kuma Ubandoman Gwandu ,Shugaban Chiyamomi na kananan hukumomi na jihar Kebbi , C.O na bataliya ta 1 Dukku Barracks na daga cikin wadanda suka saka huranni domin tunawa da mazan jiya da suka rasa ransu don kasarmu Najeriya.

A nashi jawabi yayin da ISYAKU.COM ya tuntube shi a gidansa bayan gudanar da bikin da yake shi tsohon soja ne mai mukamin Colonel, Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Rtd. Col Samaila Yombe Dabai ya yi wa Allah godiya da ya tsawaita ransu zuwa wannan lokaci . Ya kuma roki Allah ya jikan wadanda suka rasu yayin da suka tsaya tsayin daka domin tabbatar da kasancewar Najeriya kasa daya.

Ya kuma kara yi wa Allah godiya da ya cetar da rayukansu kuma ya basu lafiya kawo yanzu " Ga Alhaji Sani kanin Sule Isah,ga Col. Geoge Hans dukkansu tsoffin hafsoshin soji ne wadanda suka zo domin su nuna farin cikin da godiya ga Allah da ya kawo mu rana irin ta yau".

"Ina kuma shawartar 'yanuwanmu jami'an tsaro su dage su ci gaba domin akwai kalubale da dama wanda ke bukatar sadaukar da kai kafin a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali".

Daga karshe Yombe ya gode wa Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu bisa taimako da ya ba kungiyar tsofaffin soji na jihar Kebbi na kyautar Naira miliyan ashirin N20m da kuma umarni da ya bayar akan filaye cewa su kai korafin su ga chiyaman na Legion, shi kuma chiyaman na Legion ya sami Kwamishinan filaye a kan lamarin.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN