Shugabanin karamar hukumar Zuru da Danko wasagu sun gode wa Gwamna Bagudu

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya bayar da cheque na Miliyoyin Naira ga kungiyoyi da dama karkashin shirin ciyar da al'umma gaba tare da inganta rayuwar ta al'umman jihar Kebbi karkashin Kebbi state community and social development project (KB-CSDP).

Sakamakon haka shugabannin karamar hukumar mulki ta Zuru da Danko wasagu suka yi godiya ta musamman ga Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu da ya saka al'ummomin su a cikin wadanda suka amfana da wannan shirin.

Shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru Alh. Muhammed Kabir Abubakar ya ce zai tabbatar da cewa an cika umarnin Mai girma Gwamna bisa ka'idar yadda za'a tafiyar da aikin da aka bayar da kudaden domin a yi.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN