Labarai a yau Laraba 3/1/2018

'Yan bindiga sun sace Sarkin garin Ikulu Yohanna Kukah da ke karamar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce an sace Sarkin ne da safiyar yau Laraba.

Wata majiya ta ce 'yan bindigar sun abka fadar Sarkin ne suka yi awon gaba da shi ba tare da sun bukaci wani abu daga iyalan shi ba.

Rundunar 'yan sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce ta samu labarin bayan an sace Sarkin da safe.

Sarkin dai dan uwa ne ga babban malamin darikar katolika a Najeriya Bishop Mathew KukahWannan na zuwa bayan wasu 'yan bindiga sun hallaka Sarkin Lumana dakta Gambo Makama tare da matarsa Ruth mai dauke da juna biyu, a kauyensu mai suna 'Arak' da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna.

Jihar Kaduna dai na daga cikin sassan da suka fi fama da sace-sacen mutane don neman kudin fansa a Najeriya.

Masu zanga-zangar kin jinin hare-haren da ake kaiwa a jihar Benue sun jefi gwamnan jihar a lokacin da ya nemi yi musu jawabi .

Shaidu dai sun ce masu zanga-zangar sun bazu cikin garin Makuridi ne domin nuna rashin jin dadinsu game da hare-haren da aka kai wasu kauyuka a jihar ta Benue da ke tsakiyar Najeriya.
Masu zanga-zangar suna kira ne ga shugaban Najeriya ya dakile hare-haren da ake kai wa jihar Benue din ko kuma ya yi murabus.

Gwamnatin jihar Benue dai ta ce an kashe akalla mutum 33 a hare-haren da aka kai kauyukan jihar da ke garin Guma.

Gwamnan jihar, Samuel Ortom, dai daga garin na Guma ya fito.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Lawrence Onoja, ya shaida wa BBC cewa an fara kai hare-haren ne ranar farko ta sabuwar shekara kuma aka ci gaba da kaiwa har zuwa safiyar Talata.

Baya ga mutum 20 da kwamishinan ya tabbatar an kashe a hare-haren da ya ce makiyaya ne suka kai, an kona gidaje da dama kuma mutane da yawa sun tsere daga gidajensu.

Kawo yanzu dai kungiyar makiyaya ta Najeriya ba ta ce komai ba game da harin da aka daura wa makiyaya alhakin kaiwa.

A kwanakin baya ne dai gwmamnatin jihar Benue ta kaddamar da dokar hana kiwo a fili.

Wasu makiyayan sun yi na'am da dokar hana kiwo ta jihar Benue din yayin da wasu suka ki amincewa da ita.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, cikin kakkausan harshe, ya caccaki masu hallaka mutane ta hanyar kai hare-haren ta’addanci da sunan jihadi.

Buhari ya ce ayyukan irin wadannan masu da’awah ya nuna yadda karara suka jahilci koyarwa ta addini, domin kuwa babu yadda za’a yi Mahalicci yayi da kisan rayukan da basu jib a basu gani ba.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriyar Malam Garba Shehu ya fitar, Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne yayinda a lokuta mabanbanta, yake tataunawa da tawagar shugabancin darikar Qadiriyya na nahiyar Afrika, da kuma na Izalatul Bid’a Wa Iqamatus-Sunna a fadar gwamnati da ke Abuja.

Shugaban ya jaddada cewa jami’an tsaron kasar zasu ci gaba da aiki tukuru wajen bibiya tare da yi wa tsarin samar da tsaro ga rayuka da dukiyar al’ummar kasar garambawul, domin shawo kan dukkanin matsalolin tsaron da ke addabar Najeriya.

Don haka, magana mafi inganci bisa kwayoyin halittar Hausawa shi ne wadda wasu gungun masana su ka gudanar a kan Hausawa mazauna Sudan. Da fari, binciken ya nuna cewar kashi 40 na kwayoyin halittun Hausawa da ke zaune a Sudan sun yi daidai da na kabilun Sudan din. (Hassan et al 2008). Don haka kashi 60 ne gauraye daga kasar Hausa, 40 din kuwa su ne na usulin kakannin Bahaushe.

Read More at: https://hausa.leadership.ng/2018/01/03/shin-firaunan-kakan-bahaushe-ne-2/ Shin Fir'auna kakan Bahaushe ne ? (2)

 Shin Fir'auna kakan Bahaushe ne ? (2)


Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN