Gov. Bagudu ya gabatar da kasafin N151b na 2018 ga Majalisar dokokin jihar Kebbi

Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya gabatar wa Majalisar dokoki na jihar Kebbi kasafin kudi na 2018  ranar Talata. Gwamna Bagudu ya gabatar da kasafin Naira biliyan dari da hamsin da daya N151b a matsayin kudi da Gwamnatinsa ke shirin kashewa a shekarar 2018 ga ayyuka da wadansu bukatu na al'umman jihar Kebbi.

Da farko dai, kakakin Majalisar ya gabatar da Gwamna Atiku Bagudu ga majalisa tare da tawagarsa bisa kudurinsa na nufin gabatar da kasafin kudi na 2018 wanda wani dan Majalisa Hon. Abdullahi Shu'aibu Bunza ya gabatar da kuduri domin neman amincewar Majalisar ta yarda da kasancewar Gwamna da tawagarsa ,jami'an tsaro da 'yan jarida su kasance a cikin zauren majalisar yayin da Gwamna zai gabatar da kasafin kudin wanda 'yan Majalisaar suka aminta gaba daya.

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya yi bayani yadda jihar Kebbi ta taimaka wajen fitar da Najeriya daga kangin talauci ta hanyar shirinta na noma da dubu dubatan mutane suka amfana. Ya kara da cewa wadanda a can baya basu noma yanzu sun rungumi noma yanayi da ya haifar da karin samuwar kudaden shiga a hannun jama'a a fadin jihar Kebbi.

Ya kuma ce kamfanonin sarrafa shinkafa kamar Labana ta kara yawan shinkafa da take sarrafawa, haka zalika wani kampani ya nemi izini domin ya buda kamfanin sarrafa shinkafa a Kamba, haka zalika kamfanin Dangote zai raba irin shinkafa ga manoma a yankin Bagudo domin samun inganta harkar noma a jihar Kebbi.

Gwamna Bagudu ya ce Gwamnatinsa ta habbaka tare da inganta wutan lantarki wanda ake samu har tsawon awa 18,ya kuma ce bisa ayyuka da tsarin da Gwamnatinsa ta yi tare da kwangiloli da ta bayar nan ba da dadewa ba Yauri da Zuru za su more wuta awa 18 kamar sauran sassan jihar Kebbi.

Ya kara da cewa gwamnatinsa ta kashe fiye da N8.5b a aiyukan kananan hukumomi, haka zalika an biya gratuti da fanshon tsoffin ma'aikata wanda suka kunshi fiye da mutum 4000 wadanda ke bin kusan N500.000 kowanen su gwamnati ta biya su. An kuma kashe fiye da N10b akan harkar ilimi,gina makarantu,dakunan dalibai,sayen kujeri da gadaje da sabunta dakuna da ajujuwan dalibai a fadin jiha.

Ya ce gwamnatinsa ta kashe N250m a kowane wata wajen ciyar da daliban makaranta  sai kuma N900m da gwamnati ta kashe wajen yi wa daliban jihar Kebbi rijistan WAEC da NECO. Akwai kuma N182m da aka kashe wajen gyara tare da wadata Makarantar gona ta Zuru College of agric Zuru, N250m da aka biya wa dalibai kudin makaranta a cikin jihar da suka hada da WUFEDPOLY BK, COE Argungu, COA Zuru da sauran manyan makarantu a jihar Kebbi. Da kuma fiye da N1b da aka kashe  wa dalibai na jihar Kebbi da ke karatu a wasu makarantu a kasashen waje. Kadan kenan daga cikin jerin kasafin kudaden da aka kashe a 2017.

Daga karshe Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya mika takardun kasafin kudi na shekara ta 2018 na naira biliyan dari da hamsin da daya ga Kakakin Majalisar dokoki na jihar Kebbi domin neman amincewar Majalisar.

A zauren Majalisan, Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh Smaila Yombe Dabai tare da  kusan dukanin manbobin majalisar zartarwa na gwamnatin jihar Kebbi,shugabannin jam'iyar APC na jiha da masu ruwa da tsaki a jam'iyar APC sun halara.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN