'Dansanda ya sha duka bayan ya harbi matashi da baya dauke da makami

Matasa da suka matukar harzuka sun yi wa wani 'dansanda mugun duka bayan 'dansandan ya harbi wani saurayi a Iropora a jihar Ekiti.

EkitiDefender ta ruwaito cewa 'dansandan wanda ke aiki a chaji ofis na Igede ya harbi wani matashi ne da baya dauke da makami mai suna Mr. Ayo Oluwasusi wanda sakamakon haka ne matasan suka koya wa 'dansandan hankali ta hanyar lafta mashi na jaki.

Sau da yawa dai a Najeriya, akan sami matsaloli inda jami'an 'yansanda ke harbe mutane ko bisa kuskure ko da gangan, lamari da wani lokaci yakan zama kamar tatsuniya.
 
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN