An hana sana'ar tura baro da amalanke a jihar Lagos

Gwamnatin jihar Lagos ta aiwatar da dokar hana tura baro, da amalanke a fadin jihar. Gwamnatin ta ce ta yi haka ne bisa la'akari da cewa masu turin baro da amalanke na haddasa barazanar tsabta a fadin jihar.

A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Lagos Mr. Tunji Bello ya fitar, ya ce bisa sabon shirin gwamnatin jihar Lagos na Cleaner Lagos Initiative (CLI) kasancewar masu baro da amalanke barazana ne ga sabon tsarin tsabta a jihar Lagos.

Bello ya ce bincike ya nuna cewa masu baro da amalanke ne ke zuba shara a kwalbatoci da dare wanda hakan ke haifar da cushewar magudanar ruwa sakamakon haka ya haifar da ambaliyar ruwa a unguwanni a cikin birnin Lagos.
 
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN