Abia: zuwan mutum 100 China don koyon aikin takalma, kira ga Gwamna Bagudu

Mutum 30 cikin 100 na masu kera takalma a jihar Abia za su je kasar China domin samun horo akan yadda zasu inganta yin takalman karkashin wani shiri da gwamnatin jihar ta tsara kan taimaka wa matasa da sana'ar yi domin dogaro da kai.

Majiyarmu ta labarta mana cewa wasu mutum 30 zasu tafi China da zarar mutum 30 na farko sun dawo daga samun horon wanda zai dauki wata daya  watau kwana 30,haka za'ayi har mutum 100 su sami horon. Wasu mutum 3 wadanda ba 'yan jihar Abia bane su ma za su amfana da shirin sakamakon kwarewarsu wajen yin takalma.

Yayin da ake gabatar da addu'oi a gida gwamnatin Abia domin nema masu sa'a a kafin tafiyarsu kasar China, Gwamnan jihar Abia Dr. Okezie Ikpeazu ya bukaci su yi amfani da wannan dama domin su koyo abin da zai amfani jama'ar jihar da kasa gaba daya.

Sharhi da kira ga Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

Wannan ya tuna mini da kwatankwacin irin wannan hazaka da muke da su a nan jihar Kebbi. Akwai wani saurayi da ke kan titin  Ahmadu Bello B-kebbi, da kuma wani matashi da ke Technology incubation center a kan titin Kalgo wadanda ke kera takalma kamar a Itali aka yo su.

A nan, ina kira ga mai taimaka wa Gwamnan jihar Kebbi kan harkar taimaka wa matasa Hon. Usman Buhari Gwandu akan cewa wannan hurumin sa ne kan cewa ya matsa kaimi domin a tuna wa mai girma Gwamnan jihar Kebbi Senator Atiku Abubakar Bagudu cewa bayan taimako da ake yi wa matasa a fadin jihar, yana da kyau a tsara wani shiri na fitar da zakaru akan kananan sana'oi domin a tura su kasar waje saboda su samo ingantaccen horo.

Ta hakan bayan sun dawo, Gwamnati ta yi wani shiri da zai sa su ma su dinga koya wa wasu abin da suka koyo tunda Gwamnati ce ta dauki nauyin horar da su a kasar waje. Ta haka cikin lokaci kadan dubban matasa za su wadata da abin yi wanda zai taimaka wajen rage tabarbarewar tarbiyya da mutuncin rayuwa a tsakanin matasa a unguwanni.

Isyaku Garba


Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN