Yombe ya yi kira ga manoma su biya bashin da suka karba domin wasu su amfana

Al'umman garin Dirin Daji da Yauri sun kai koke ga Mai girma Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai sakamakon sammaci da aka kai masu bisa gazawar wasu wajen biyan bashin da aka basu na Manoma karkashin shirin Anchor borrower a bara.

Amma a nashi jawabin ga tawagar, Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe ya ce rashin biyan wadannan kudaden shi ya jawo hankali a kan lamarin, domin tun shekara biyu da suka gabata muke ta gaya wa mutane wadanda suka sami wannan tallafin su yi kokari su biya kamar yadda aka shirya saboda wadanda basu samu ba su ma su samu.

Yombe ya kara da cewa jama'a sun ci gaba da jan kafa a lamarin duk da albarka da aka samu a noman da aka yi, ya kamata a biya kudinnan tun bara, kuma Gwamnati ba za ta sa ido tana kallon wadanda suka karbi kudin suka amfana da su kuma basu yi kwazon biya ba, kuma sai idan sun biya ne za'a yi amfani da kudin domin wasu su ma su amfana.

Alh. Samaila Yombe ya yi tuni ga jama'a da suka karbi bashin akan muhimmancin biyan bashi a Musulunci da kuma sharudda da ke kunshe akan lamarin bashi kamar yadda Musulunci ya tanada.Sakamakon haka Yombe ya kara rokon jama'a cewa su yi kwazo su daure su biya bashin domin alhairin ya zagaya a cikin jama'a.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN