Uba da amarya sun kone duwawu da al'auran dan shekara 2 domin ya cinye alala

Hukumar da ke kula da fatauci da cin zarafin yara ta kasa NAPTIP ta kama wani magidanci 'dan shekara 43 mai suna Ayo da matarsa 'yar shekara 30 mai suna Khadijat bayan sun kona al'aura da duwawun yaro 'dan shekara 2 da wuta a Kuje na birnin tarayya Abuja.

Yaron 'dan shekara biyu wanda 'da ne ga Ayo ya yi rarrafe ne zuwa cikin kichin inda ya dauki kulli 'daya na alala wanda ya gani, sai ya dauka a cinye domin ba a bashi abinci ba daga safe har zuwa karfe 2 na rana.

Sakamakon haka Ayo da Khadijat suka azabtar da yaron ta hanyar kona masa al'aura da duwawu. Wata majiya ta labarta cewa Ayo ya karbo yaron ne daga hannun mahaifiyarsa wacce tsohuwar matarsa ce.

Wani makwabci ne ya shaida wa hukumar ta NAPTIP lamarin wanda su kuma suka zo suka kama Ayo da amaryarsa Khadijat kuma suna gudanar da bincike akan lamarin yayin da aka tsare Ayo da Khadijat a Kurkukun Kuje a birnin Abuja.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN