Taron ECOWAS na 52 a Najeriya: Buhari ya bukaci a tallafa wa matasa

Shugabannin kasashen yammacin Africa na ECOWAS sun fara gudanar da taron hadin kai na kasashen wannan yanki a karo  na 52 inda suka mayar da hankali akan harkokin Siyasa, tattalin arziki da tsaro.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi bayani akan mahimmancin hadin kai da kyakyawar alaka da juna domin hakan zai inganta harkar samar da tsaaro.

Kazalika Shugaba Buhari ya tabo batun cinikin Bayi a Libya inda ya ke cewa, 'tallafawa matasa da samar da ayyukanyi zai taimaka wajen dakile kwararar Bakin-haure da ke jefa rayuwarsu cikin hatsari a libya.'

Shugabannin ECOWAS za kuma su yi nazari kan hanyoyin shawo rikicin siyasar Togo da Guinea Bissau, da kuma samar da sauye-sauye kan ayyukan Kungiyar.

Taron dai ya samu halartar shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki da wakilan Majalisar dinkin duniya da kuma tsoffin shugabannin kasashen Afirka.


Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN