Soja ya harbe kanshi sakamakon rashin canjin wajen aiki

Wani soja mai suna Samaila Gabriel ya bindige kansa har lahira a jihar Yobe. Sojan mai lambar aiki 09NA/63/2867 ya bindige kansa ne sakamakon rashin amincewar kwamandan sa domin ya canja masa wajan aiki kamar yadda Samaila ya roka.

Daya daga cikin abokan Samaila ya shaida wa TheCable haka ,ya kuma kara da cewa an tura Samaila aiki a Yobe ne shekara uku da suka gabata.

An adana gawar Samaila Gabriel a Asibitin Sani Abacha da ke garin Damaturu a jihar ta Yobe.

Rahotanni sun nuna cewa babu wani bayani kawo yanzu daga hukumomin soji.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN