Rikicin Sabon garin Illo, Gwamnati ta bukaci Fulani da Manoma su fice daga gurin da ake rigima a kai

Gwamnatin jihar Kebbi ta ba Fulani da Manoma a kauyen Sabon gari Illo zuwa 12:00 pm Juma'a 22/12/2017 domin su fice daga guri da ake rikici a kai su kuma jira mataki da Gwamnati za ta dauka.

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai bayan karbar umarni daga Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya ce Fulani da Manoma a kauyen Sabon gari su fice daga gurin da ake rigima a kai domin a tabbatar da zaman lafiya bayan wani hargitsi da ya yi sanadin salwantar rayuwar mutum daya .

Ranar Talata ne aka sami wata hatsaniya da ya yi sanadin mutuwar mutum daya, tare da bacewar wani mutum daya haka zalika mutum biyu sun sami rauni a kauyen na Sabon gari da ke karkashin rikon Illo.

Dukan bangarorin suna da har zuwa karfe 12:00 na ranar Juma'a domin su kaurace ma gurin bisa umarnin na Gwamnati.

Yombe ya ce Gwamnati ta dauki matakin ne domin a kaurace ma yanayi da zai iya kai ga salwantar rayuka da dukiyar al'umma kuma domin a tabbatar da yanayi na ingantaccen tsaro a wannan yankin.


Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN