Ma'aikaci ya kashe kansa sakamakon rashin albashi wata 12

Rahotanni da suka fito daga jihar Kogi sun nuna cewa wani ma'aikacin Gwamnatin jihar Kogi mai suna  Abdullahi Uye Zhiya ya kashe kansa bayan ya sha guba da ya yi sanadin ajalin sa a Oguma na karamar hukumar Bassa da ke jihar Kogi.

Abdullahi Uye Zhiya shi ne babban mai ajiye kayaki na Universal Basic Education Board Oguma. Bayanai sun nuna cewa marigayin yana cikin wadanda aka dakatar da su daga aiki kuma yana bin Gwamnati albashin wata 12.

Wata majiya taa ce marigayin ya koka kwarai akan yadda rashin albashin ya sa baya iya ciyar da iyalinsa kuma sadin haka aka kore yaransa guda hudu daga makaranta sakamakon rashin biyan kudin makarantar.Haka zalika bayanai sun nuna cewa Abdullahi yana fama da rashin lafiya wadda ya karu sakamakon rashin albashi balle ya sayi magani.

A jihar Kogi dai a cikin wata biyu wannan shi ne rahotun mutum na uku da ya kaashe kansa sakamakon rashin biyan albashi da tankade da rairaya da Gwamnatin jihar ta yi.

 
**************************************** Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com **************************************** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
Ma'aikaci ya kashe kansa sakamakon rashin albashi wata 12 Ma'aikaci ya kashe kansa sakamakon rashin albashi wata 12 Reviewed by on December 01, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.