Labaran Duniya Alhamis 14/12/2017 (Yamma)

Rundunar 'yan sandan jihar Kogi da ke Najeriya ta ce ta kori jami'anta uku da take zargi da laifin fatauncin wiwi.

Kakakin rundunar ASP William Aya ya tabbatar wa BBC cewa jami'an hukumar hana sha da fataucin kwayoyi, NDLEA ne suka kama 'yan sandan a watan Nuwamba lokacin da suke yin rakiya ga wata mota dauke da buhu 30 na wiwi a Lokoja, babban birnin jihar.

Ya kara da cewa hukumar NDLEA ce za ta gurfanar da su a gaban kotu
A cewar ASP Aya, rundunar 'yan sanda ba za ta lamunci duk wani jami'inta da zai bata mata suna ba.
Ana zargin 'yan sandan kasar da yin kaurin suna wajen aikata laifukan da suka kamata su hana aikatawa, ko da yake sun sha musanta zargin.

An gurfanar da matan da ake zargi da kashe mijinta, Maryam Sanda da mahaifiyarta da kuma 'yan uwanta a gaban kotu.

A wannan karon, an gyara tuhumar da ake yi mata inda aka tuhume ta da kashe mijinta, Bilyaminu Bello Halliru, ta hanyar daba masa wuka da sauran makamai masu hatsari.

Sai dai Maryam ta musanta tuhumar.Har ila yau an tuhumi mahafiyarta, Maimuna Aliyu da 'yan uwanta Aliyu Sanda da Sadiya Aminu da laifin goge hujjar kisan kai domin kubutar da Maryam Sanda daga fuskantar da shari'a kan laifin kisan kai.

'Yan uwan Maryam din dai sun musanta tuhumar da aka yi masu.

Da aka fara gurfanar da Maryam dai, lauyan rundunar 'yan sandan birnin tarayyar Najeriya, Abuja, James Idachaba, ya nemi kotun ta ba shi lokacin domin ya gyara tuhumar da ake yi wa wadda ake zargin bisa sabbin bayanai da rundunar 'yan sandan birnin ta samu.

Yayin zaman kotun na ranar 7 ga watan Disamba domin jin sabuwar tuhumar, sai lauya James ya ce bai samu ya bai wa sauran wadanda ake tuhuma da aikata laifi kan lamarin sammaci ba.

Saboda haka sai kotun ta ba shi mako daya domin ya gabatar da sauran wadanda ake zargi da aikata laifi a lamarin.

Tsohon Shugaban kasa Yakubu Gowon, ya yi da-na-sanin rashin maida Jos a matsayin babban birnin tarayyar Nijeriya.

Gowon, ya ce ya ki aiwatar da haka ne, don kada a ce ya cika tsananin nuna son yankin sa ko kuma yi wa sauran yankunan Nijeriya mugunta.

Tsohon shugaban kasar, ya bayyana haka ne a wurin bikin cika shekaru 26 da maida babban birnin tarayyar Nijeriya daga Lagos zuwa Abuja.

Ya ce saboda ya na kallon garin Jos ya yi kusa da mahaifar sa, shi ya sa bai maida shi ya zama birnin tarayya Nijeriya ba.

Gowon ya nuna takaicin sa a kan cewa, duk da shi ne ya fara nuna Abuja ce ta fi dacewa ta zama birnin tarayya, amma ba a sanya wa wani titi ko gini sunan sa ba, har sai da ya yi wa tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida korafi.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, ya maida martani game da umurnin kotun daukaka kara na maida shi kotun da’ar ma’aikata domin fuskantar tuhume-tuhume 3 da su ka shafi karya wajen bayyana kadarorin sa.

A baya dai Kotun da’ar ma’aikata ta wanke Bukola Saraki, bisa zargin sa da aikata laifuffuka 18, da su ka hada da karbar albashi fiye da daya, da mallakar dukiyar da tafi karfin albashin sa, da rashin bayyana wasu kadadori da hannun jari da ya mallaka, da kuma mallakar asusun ajiya a kasashen waje da sauran su.

Mai magana da yawun Sanata Bukola Saraki Yusuf Olaniyonu, ya ce tun da kotun daukaka karar ta yi watsi da zarge-zarge 15 cikin 18, ya na da yakinin cewa sauran ukun ma za a yi watsi da su, domin a cewar sa, Saraki bai aikata wadannan laifuffuka ba.

Olaniyonu ya kara da cewa, lauyoyin Saraki su na jiran cikakken bayani daga kotu, bayan sun duba a tsanake za su dauki matakin da ya dace.

Majalisar wakillai ta kafa kwamitin da zai binciki kamfanin NNPC bisa da zargin kin zuba kudaden da su ka kai akalla Naira Biliyan 50 a cikin asusun bai-daya na gwamnatin tarayya watau TSA.

Sai dai ‘yan kwamitin sun bayyana cewa, maimakon kamfanin NNPC ya zuba kudaden inda aka umurce shi, sai su ka karkatar da su zuwa bankunan ‘yan kasuwa.

Zargin dai ya fito ne ta bakin shugaban kwamitin binciken, kuma dan majalisar wakilai daga jihar Kano Alhaji Abubakar Nuhu Danburam, yayin da ya ke zantawa da manema labarai.

Sai dai jami’an kamfanin NNPC cewa su ka yi, sun yi hakan ne da sanin shugaba Muhammadu Bahari, inda shi ma babban bankin Nijeriya ya gasgata hakan.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN