Labaran Duniya Alhamis 14/12/2017 (Safe)

Kungiyoyin kare hakkin bil'dama da 'yan jarida da kuma jami'an MDD sun riga sun tattara bayyanai daga 'yan gudun hijira da suke samun mafaka a kasar Bangladesh akan cin zarafi mai tayar da hankali, da suke zargin jami'an tsaron Myanmar sun yi a jihar Rakhine. 

Sai dai wannan shi ne karon farko da ake samun binciken da ya samar da cikakken bayyani kan yawan musulmi 'yan Rohingya da aka kashe a tashin hankalin da ya barke sakamakon jerin hare haren da mayakan sa kai yan Rohinja suka kai a watan Augustan daya gabata
Lamarin ya sa sojoji suka kai mummunan farmakin da MDD ta bayyana a matsayin kawarda wata kabila daga doron kasa.

Kungiyar agaji ta likitoci ta Medicine san frontiers ta gudanar da bincike guda shida a watan daya gabata a sansanonin 'yan gudun hijira , inda ta yi magana da mutane dubu biyu da dari biyar .


Ta gano cewa mace macen da aka yi musaman tsakanin yara a mafi yawan lokuta ya zarta yadda ake tunani kuma kashi sabain cikin dari na mace macen sun faru ne a tashin hankalin, da ya faru.
MSF ta kuma ce akasarin su sun rasa rayukansu ne daga raunukan da suka ji daga harbin bindiga, adadin da ya zarta kiyasin da aka fitar tun farko.

Sai dai wannan rahoton zai karfafa kiraye kirayen da wasu suke yi akan cewa ya kamata a binciki hukumomin Myanmar game da zargin cin zarfin bil'adama.

Rundunar sojin Myanmar din dai ta riga ta gudunar da bincike kan zargin da ake yi ma sojojin kasar kuma ta ce sojojinta basu aikata laifi ba.

Har yanzu masu bincike daga MDD da kuma kungiyoyi agaji basu sami damar zuwa jihar Rakhine ba.


Shugabannin Kasashen Musulmin duniya sun bukaci mutunta gabashin Birnin Kudus a matsayin babban birnin Falasdinu da kuma bayyana Amurka a matsayin wadda ta rasa gurbin ta na mai shiga tsakani wajen sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya.

Shugabannin sun kuma yi watsi da matsayin Amurka na bayyana Birnin Kudus a matsayin babban birnin Israila.

Wadannan na daga cikin matsayin da taron shugabanin ya amince da su a kasar Turkiya.

Shugaban Turkiya Racep Tayyib Erdogan, ya buƙaci dukkanin ƙasashe masu adalci da su girmama dokokin duniya da kuma ɗaukan gabashin Ƙudus a matsayin babban birnin Falasɗinu.

Erdogan ya ƙara da cewa ƙasashen na musulunci ba za su yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin tabbatuwar wannan buƙata ta su.

Mahalartar taron sun ce ba za ta saÉ“u ba, da ayyanawar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Ƙudus, a matsayin babban birnin Isra’ila.

Sashen dake lura da wanzuwar zaman lafiya da lamarin makamai a Afrika na Majalisar Dinkin Dunya (UNREC) ya bayar da haske dangane da yadda makamai marasa rijista ke yawo a fadin tarayyar Nijeriya, inda ta bayyana cewa sama da makamai guda miliyan 350 ke hannun jama’a ba tare da bin ka’idar mallakarsu ba.

A cewar Majalisar ta dinkin duniyan, daga cikin makamai miliyan 500 wadanda basu da rajista da ake da su a fadin Afirka, kaso 70% suna hannun ‘yan Nijeriya ne. wand aba karamin lamari bane mai tayar da hankali.

Daraktan Sashen na ‘UNREC’, Mista Anselme Yabouri ne ya bayyana wannan adadin a wurin wani taron kara wa juna sani kan tsaro da gudanarwa da ke gudana a Babban Birnin Tarayya da ke Abuja, taro wanda kuma sashen na UNREC tare da hadin gwiwar Kwamitin Shugaban Kasa mai lura da kananan makamai ‘PRESCOM’ suka dauki nauyin shirya wa.

Yabouri ya bayyana cewa, Nijeriya cike take da makamai marasa rajista, wadanda aka shigo da su ta barauniyar hanya a munafunce, kuma suke a hannun mutanen da ba su dace ba a fadin kasar nan.
“Kutse da shigowa da makamai ba bisa ka’ida ba na taka muhimmiyar rawa wurin rashin tsaro a Afirka, wanda ba kawai yana zama barazana ne ga gwamnatoci ba, hatta ga miliyoyin rayukan al’umman da ke yankin.

Nijeriya kasa ce da ke da kaso mafi tsoka a irin wannan, don haka kasar ke fuskantar barazana na tsaro. Kuma an samu hakan ne a Nijeriya sakamakon rikice-rikicen da suka afku a kasashen Libiya da Mali tare kuma da wasu rikice-rikicen cikin gida a wasu sassan kasar, kamar wanda ke faruwa a Arewa maso Gabas, Neja Delta da kuma wasu sassan kudancin Kasar.

“Masana sun jaddada cewa akwai makamai gudamiliyan 500 wadanda suke hannun jama’a a Afirka, wadanda kuma ba a bi ka’ida wurin mallakarsuba. Kaso 70% na wannan adadi suna Nijeriya ne.

Wannan adadi ne mai tsoratarwa da ba firgitarwa, wanda idan har ba a dauki mataki ba, za a samu gagarumar matsala a fadin kasar nan ba da jima wa ba.” in ji shi

Yabouri ya kara da cewa; “Kamar yadda wanda na gada ya fadi a irin wannan taron a shekarar da ta gabata, samar da dokoki masu inganci, bin hanyoyi don kiyaye wa kadai ba za su iya wanzar da zaman lafiya ba. Dole ana bukatar jajircewa da mayar da hankali kafin a iya magance irin wannan matsalar.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN