Kotu ta hana belin Maryam, 'yansanda sun hada da mahaifiyarta cikin tuhuma

Wata babban Kotun tarayya a Jabi na birnin tarayya Abuja ranar Alhamis ta ki ta bayar da belin Maryam Sanda wacce hukumar 'yansanda a birnin Abuja ta gurfanar a gabanta bisa zargin kashe Mijinta Bilyamin Bello a cikin watan Nuwamba kuma Kotu ta bayar da umarni a ci gaba da tsare Maryam a gidan yari har zuwa zaman Kotun na gaba.

Hukumar 'yansanda ta gurfanar da Maryan akan laifuka guda biyu da suka hada da "kisan kai ta hanyar kashe mijinta da kwalba ta hanyar daba masa fasashshen kwalban a kirji tare da sanin cewa hakan zai kashe shi" .

Jami'in 'dansanda mai gabatar da kara CSP James Idachaba ya shaida wa Kotun cewa hukumar 'yansanda ta yi kwaskwarima ga karar da ta shigar inda hukumar ta hada da mahaifiyar Maryam watau Maimuna Aliyu Sanda da wasu mutum biyu a cikin tuhumar domin su fuskanci shari'a.

Ya kara da cewa yunkurin 'yansanda na mika wa wadanda ake tuhumar takardar tuhuma ya ci tura kawo yanzo sakamakon haka ya nemi Kotu ta dage shari'ar har ranar 14 ga watan Disamba domin a sami sukunin gabatar da dukan wadanda ake tuhumar a gaban Kotu domin su fuskanci shari'ar gaba daya. 

Daga Isyaku Garba

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
Kotu ta hana belin Maryam, 'yansanda sun hada da mahaifiyarta cikin tuhuma Kotu ta hana belin Maryam, 'yansanda sun hada da mahaifiyarta cikin tuhuma Reviewed by on December 07, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.