Jihar Kebbi: Karanta abin da aka ce akan Gwamna Atiku da Yombe

An wayi gari ana ganin ababe kala kala dangane da kalamai da wasu bayin Allah ke rubutowa a shafin yanar gizo da sunan fadin ra'ayin bakin su.Daga ciki kuma akwai suka wacce akwai ta fahimta akwai kuma ta kazafi da neman ganin laifi da gangan akan Gwamnatin jihar Kebbi tare da Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi wanda aka auna bisa lissafin kuskure daga masu korafe-korafe sakamakon rashin samun bayani da ya kamata ace sun samu kafin su yi korafe-korafen.

Su dai wadanda suka rubuta korafe korafe akan cewa Gwamnatin jihar Kebbi bata biya wa dalibai kudin makaranta ba bai san lamarin da jihar Kebbi ke ciki bane, a ina kuke lokacin da Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya biya fiye da N100m kasancewar kudin
 Karanta hjja a nan >>
makaranta na dalibai 'yan asalin jihar Kebbi da ke karatu a UDUS da COE Sokoto ? idan kana da aboki ko 'dan uwa a wadannan makarantun ai sai ka tambaya ka ji.Haka zalika dalibai na makarantun gaba da Sakandare na jihar Kebbi an biya kudaden makarantar su.

Wadanda ke suka akan kiyon lafiya ina kuke lokacin da Gwamna ya bude Asibitin kwararru na jiha da ke garin Kalgo kuma aka samar da wadatattun Likitoci da wasu karin kwararru da suka zo domin taimaka wa dubannin 'yan jihar Kebbi da ke fama da matsaloli daban-daban na rashin lafiya kuma cikin sauki ?.

Don Allah a ina ka ga Mai girma Gwamnan jihar Kebbi ya kwashi kudin jiha ya kai ya boye ko ya gina wani gida ko Otel? ko mataimakinsa ?...haba idan za ka yi zargi ai sai ka yi zargi mai ma'ana. Idan baka sani ba tau ka sani daga yau cewa Gwamnatin jihar Kebbi karkashin Gwamna Atiku Bagudu da Mataimakinsa Samaila Yombe Gwamnati ce da ba'a taba samun irinta ba a tarihin jihar Kebbi bisa  hujjar cewa Gwamnati ce da ta kare darajar Ma'aikatan jihar Kebbi sakamakon biyan albashi kafin wata ya kare kuma babu ma'aikacin da ke bin Gwamnati bashi albashi ko na wata daya .

Gwamnati ce da ba ta bayar da kwangila sai ta tabbatar akwai kudin da za'a biya 'dan kwangila a kasa kuma matukar ya kare kwangilar sai a jibge masa kudinsa a kasa.Sakamakon haka babu wani 'dan kwangila da ke bin wannan Gwamnati bashin ko kwabo.

Gwamnati ce da bata yi wa kowa bita da kulli kamar yadda wadansu Gwamnatoci suka yi ta yi wa Ma'aikat da 'yan kasuwan jihar Kebbi kafin Allah da kanshi ya gaji da su kuma ya sauya lamarin domin ya kawo sauki cikin rayuwar al'ummar jihar Kebbi.

Gwamnati ce da ita ce ta farko da ta fito da daraja tare da martabar manoman jihar Kebbi ta hanyar ba su bashi domin a mutunta sana'arsu  su ma su sami ingancin rayuwa. Sakamakon haka bayanai na kididdiga sun nuna cewa wadanda suka sami zuwa aikin Hajji a bana daga jihar Kebbi kashi 80 Manoma ne.

Gwamnati ce da ta ke iyakar kokarin ta domin tabbatar da tsaro a fadin jiha sakamakon haka aka kafa Kwamiti karkashin kwararren tsohon Janar na soja mai murabus Janar Dan Hanne wanda ya sa dubannin barayi da 'yan fashi suka kawo kansu suka tuba sakamakon haka tsaro ya kara inganta a jihar Kebbi.

Gwamnati ce da ta fito da kwarjini da martabar kowane 'dan jihar Kebbi a fadin Najeriya da fadin Duniya sakamakon shirin noman shinkafa, idan ba ka fita a wajen jihar Kebbi , to ka bari wadanda ke fita wajen jihar su gaya maka yadda ake kiransu "Yan noman shinkafa" amma a da me ake kiran 'yan jihar Kebbi kuma waye ya san ka ?.

Yanzu saboda Allah idan bancin ba'a biyan haraji domin amfani da Facebook ta yaya wani zai kirkiro zargin rashin ma'ana da ragowa akan Mai girma Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai cewa ya ci kudin aiki da aka bayar domin mutanen Zuru ? haba ! ta yaya za ka kalli wannan Dattijo ka yarba masa sharri kamar a Duniya za a tabbata ? waye ya bayar da kudin ? nawa ne yawan kudin ? aikin miye da miye aka bukaci a yi da kudin kuma aka cinye ?...shin aikwai tsoron Allah a cikin wannan tunani ?.

Idan har babu amsar wadannan tambayoyi da muka zana a sama, yana da kyau in lurar da kai wani abu, matukar zuciyarka bata raya maka alkhairi akan shugabannin ka lallai ala kulli yaumin za ka kasance cikin damuwa da wahala domin har abada za ka dinga ganin cewa shugabanni azzalumai ne alhalin tunanin ka ne ya zalunce ka kai kuma ka kaddamar da zalunci akan kanka ta hanyar aiwatar da karkataccen tunaninka.

Alh Samaila Yombe Dabai Dattijo mai nufin alkahairi ga mutanen Masarautar Zuru da Yauri ne tare da gabadayan 'al'umman jihar Kebbi,mutum mai hidima da jama'a a Birnin kebbi ,gida da ofis haka zalika idan ya zo Zuru ko Yauri inda bai sami zuwa ba kuwa yakan yi sako zuwa mazabu. Amma idan alkhairin sa bai kai hannun ka ba yanzu sai ka 'dan yi hakuri kadan nan gaba ba da dadewa ba zai kai gareka idan Allah ya yarda .Saboda haka bai kamata ka yanke hukunci kai tsaye ba domin wani abu bai shiga hannun ka ba yanzu.

Shi ya sa yana da kyau a yi biyayya ga shugabanni kamar yadda yake a Musuluci haka zalika bahaushe ya ce bin na gaba bin Allah, ka yi hakuri ka yi biyayya ga shugabannin ka a yanzu mai yiwuwa kai ma za ka zama shgaba a nan gaba, abin da ka yi kaima sai a yi maka.Ka kwan da sanin cewa jihar Kebbi ta dace da shugaba karkashin jagorancin Gwamna Sanata Abubakar Atiku Bagudu da Mataimakinsa Alh. Samaila Yombe Dabai , Dattijai masu nufin alkhairi a gare ka.

Daukan nauyin wallafawa:
Daga Dept. Gov. Media Team

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN