Jikewar kasa ya haifar da yiwuwar rugujewar benen makaranta a Badariya

Wani ibtila'i ya sami Makarantar Annur Nursery da Pimary da ke unguwar Badariya kan mashigar gidan Gari Malam sakamakon tsatssagewa da wani ginin makarantar mai hawa daya ya yi kuma haka ya haifar da barazanar yiwuwar rugujewar ginin.

Bayanai da ISYAKU.COM ya samu ya nuna cewa hakan ya faru ne sakamakon wani gyara da aka yi na bututun ruwa da ke shimfide a karkashin kasa, dalilin haka ya sa wani dadadden bututun ruwa da baya aiki ya fara fitar da ruwa ta karkashin kasa'

Sannu a hankali karkashin kasa da ke ginin sashen wannan gini mai hawa daya na makarantar ya jike kuma kasar ta yi sanyi, sakamakon haka kasar ta tsage wanda hakan ya haifar da tsagiwar ginin.

A tattaunawa da ISYAKU.COM shugaban Makarantar Mal. Abdullahi Bagudu ya shida mana cewa jiya da dare ne lamarin ya faru, ya kara da cewa saura kasa da wata daya 'daliban Makarantar su dawo daga hutu, kuma yana tattaunawa da injiniyoyi masana akan harkar gine-gine domin samun shawara.

Bayanai sun nuna cewa hukumar Makarantar ta kammala tsari domin gabatar da wannan lamari ga Gwamnatin jihar Kebbi ta hannun babban Daraktan kula da bayar da taimakon gaggawa na jihar Kebbi watau State Emergency Management Egency SEMA,  Alh. Sani Dododo.

Isyaku Garba.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN