Hotel da kungiyar Izala ta gina a Abuja

Kungiyar Izala ta gina wani katafaren Hotel a birnin Abuja, lamari da shugaban ta Alh. Abdullahi Bala Lau ya ce sun gina Hotel 'din ne bisa bukatar haka.

Bala lau ya shaida wa BBC cewa  "To a matsayinmu na kungiyar addini muna da wadansu bukatu da suka sha mana gaba wadanda ya kamata a ce mun yi su kafin mu kai wannan,"

Har ila yau, malamin ya ce kafin su gina otel din akwai wata jami'a da kungiyar take kokarin samarwa da kuma kungiyar tana da makarantu da dama wadanda ta gina.


Hakazalika ya ce a matsayinsu na kungiyar addini ba zai yi wu su gina masaukin baki kuma "mu bari a rika saba wa Allah a cikinsa ba."

Ya kuma kara da cewa Malamansu na bukatar masauki a birnin Abuja kuma suna bukatar wuri mai tsafta.

**************************************** Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com **************************************** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
Hotel da kungiyar Izala ta gina a Abuja Hotel da kungiyar Izala ta gina a Abuja Reviewed by on December 02, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.