Hatsarin babur: Bashir Gwandu abokin Yusuf Buhari na a sume har yanzu

Babban abokin Yusuf  'dan shugaba Muhammadu Buhari watau Bashir Gwandu yana nan a sume har yanzu a Asibitin Cedarcrest Hospital sakamakon hatsari da ya samu tare da Yusuf a Gwarimpa na babban birnin Tarayya Abuja ranar Talata 26 ga watan Disamba.

Rahotanni daga kafafen labarai da dama sun nuna cewa Yusuf yana kokarin tsere wa Bashir ne a wani gudun babura Power Bikes sakamakon haka babur ya kwace masa lamari da ya sa suka yi karo kuma suka fadi.

Bayanai sun nuna cewa Yusuf ya karye, kuma ya sami raunuka a kan sa, amma an yi masa aiki kuma yana samun murmurewa.


Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
Hatsarin babur: Bashir Gwandu abokin Yusuf Buhari na a sume har yanzu Hatsarin babur: Bashir Gwandu abokin Yusuf Buhari na a sume har yanzu Reviewed by on December 29, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.