'Dan fashi ya kai kanshi chaji ofis bayan ya bindige abokinsa dan fashi bisa kuskure

Saurayi mai shekara 25 'dan fashi da makami mai suna ThankGod Smith ya kai kanshi ga hukumar 'yansanda bayan ya bindige wani abokinsa dan fashi mai suna Peter Napoleon mai shekara 23 har lahira yayin da suke yi wa wani mai suna Francis Chibueze fashi a kauyen Azikoro na hanyar Baker a Yenagoa na jihar Bayelsa.

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar 22 ga watan Disamba 2017, amma bayan 'yansanda sun fara bincike sai ThankGod Smith ya kawo kan shi chaji ofis na Azikoro ranar 23 ga watan Disamba 2017 inda ya yi bayani cewa shi ne ya bindige abokinsa bisa kuskure.

Haka zalika ThankGod Smith ya kai 'yansanda a wani kangon gida a kauyen na Azikoro wajen da suka boye makamin da suka yi amfani da shi wajen fashi.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN