Argungu United na Argungu ta lallasa New star na B-kebbi ci 3-2, ta dauki kofi

Isyaku Garba |

An kammala gasar wasan kwallon kafa na cin kofin Dr Muh'd Sanusi wanda kungiyar kwallon kafa ta jihar Kebbi ta shirya karo na 5 inda kungiyar kwallon kafa ta New stars FC na Birnin kebbi ta sha kashi a hannun kungiyar Argungu United FC da ci 3-2.

Duka kungiyoyin sun taka laida gwanin burgewa, yayin da Argungu United ta yi ta kai hari a gidan Newstar FC ita kuma Newstar FC ta yi ta kuren kada kwallo a ragar Argungu United.

A takaitaccen jawabi da ya yi a wajen kwalon, Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya ce Allah ya yi wa jihar Kebbi gata da ya ba mu Gwamna kamar Mai girma Gwamna Sanata Abubakar Atiku Bagudu wanda masoyin kwallon kafa ne kuma bisa wannan dalili ne ya bayar da kwangilar gina Filayen kwallo a Masarautu hudu da ke jihar Kebbi.

Yombe ya yaba wa Gwamna Atiku Bagudu bisa shirye shiryen sa na taimaka wa Matasa, ya kara da cewa Matasa su ne ginshikin al'umma sakamakon haka ne Mai girma Gwamna Atiku Bagudu ya bayar da muhimmanci na musamman akan harkokin taimakon matasa.

Ya kuma bukaci matasa su ba Gwamnati goyon baya kuma su kasance masu dogaro da kansu wanda a shirye gwamnatin Mai girma Gwamna Atiku Bagudu take domin tallafa wa matasa.

An gabatar da kyautuka ga zakaru da wadanda suka yi fice a harkar kwallon yayin da aka ba kungiyar Argungu United kyautan Kofi da tsabar kudi N70.000. New star FC na Birnin kebbi ta tashi da karamin kofi da tsabar kudi N50.000.

Manyan baki da suka halarci wasan kwallon sun hada da Kwamishinan wasanni Hon. Abubakar Imam, Perm, Sec youth & sports Alh Garba Hussaini Mungadi, Mai girma Wazirin Gwandu Alh. Abdullahi Umar, Daraktan wasanni Alh. Usman Umar Ladan tsohon mai tsaron gida na kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Peter Rufa'i da sauran manyan baki.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN