• Labaran yau

  An tsinci jarirai da aka haifa aka yar a B-kebbi da Gulumbe (Hotuna)

  An tsinci wadansu jarirai guda biyu wadanda aka haife su kuma aka yar a wasu sassa a jihar Kebbi .An tsinci jariri da aka saka a cikin laida kuma aka jefar a gefen ofishin JNI a garin Birnin kebbi yayin da dayan aka samu a Bawada a cikin garin Gulumbe.

  Wani babban jami'i a ofishin na HIZBAH na jihar Kebbi ya shaida wa ISYAKU.COM tabbacin haka a wata tattaunawa ta wayan salula.Jami'in ya ce "akwai karin wadansu guda biyu da aka tsinta a Argungu da kuma wanda aka tsinta a garin Gwandu"

  Idan baku manta ba, kwanakin baya mun ruwaito maku labarin yadda wata yarinya ta haifi jariri kuma ta yar da shi a garin Yauri a jihar Kebbi.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An tsinci jarirai da aka haifa aka yar a B-kebbi da Gulumbe (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama