An daura auren 'ya'ya Mataimakin Gwamnan jiha Kebbi Samail Yombe (Hotuna)

Isyaku Garba |

Da ranar yau Juma'a bayan Sallah aka gudanar da daurin auren 'ya'yan Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai su biyu Rakiya Samaila Yombe da Ibrahim Muhammed sai Basira Samaila Yombe da Tyron B. Abdulkareem a babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi (Central Mosque wanda ya sami halarcin Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu.

Haka zalika manyan mutane da suka halara sun hada da Ministan shari'a Abubakar Malami SAN ,Sanata Adamu Aliero,Sanata Bala Ibn Na'Allah, Mataimakin Gwamnan jihar Sokoto Alh. Ahmad Aliyu Sokoto, Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara ,Kakakin Majalisar Dokoki na jihar Kebbi ,Shugabannin Kananan hukumomi na Danko wasagu da sauran Manyan baki.

A nashi jawabi yayin kammala liyafar cin abinci da aka gudanar a Presidential Lodge Birnin kebbi, Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu ya roki Allah ya ba Ma'auratan hakurin zama da juna tare da albarka a zamantakewarsu.Haka zalika shi ma Ministan shari'a Abubakar Malami SAN, ya roki Allah ya ba Ma'auratan zaman lafiya.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN