An cafke wani mutum da mataccen jariri kulle a cikin laida

Ajiboye Emmanuel wani mutum ne 'dan shekara 42 da aka kama dauke da matacen jariri a cikin laida yayin da ya shiga wata mota da ta taso daga tashar Sapade a jihar Ogun.

Wata majiya ta labarta cewa ranar 22 ga watan Disamba ne lamarin ya faru bayan wasu fasinja sun jawo hankalin 'yansanda sakamakon wani mumunan wari da ya dinga fitowa daga laidar da Ajiboye ya shiga motar da ita.

Bayan isowar 'yansanda sun bincika abin da ke ciki sai suka gano cewa mataccen jariri ne a ciki, Amma Ajiboye ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa Lagos ne domin ya bizine jaririn.

Kwamishinan 'yansanda na jihar Ogun Ahmed Iliyasu ya tabbatar da cafke Ajiboye, ya kuma bayar da umarni cewa a mika binciken zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
An cafke wani mutum da mataccen jariri kulle a cikin laida An cafke wani mutum da mataccen jariri kulle a cikin laida Reviewed by on December 26, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.