Ambasadan Libya a Cameroon ya sha dukan ramuwar gayya a hannun matasa

Wani babban Edita na jaridar Sun Newspaper Peter Agba ya ruwaito cewa wasu Matasa da suka harzuka akan irin ababen da ake yi wa bakaken fata 'yan Afrika a Libya sun lakada wa Ambasada na kasar ta Libya a Cameroon mugun duka domin ramuwar gayya.

Kasar Libya dai ta tsunduma cikin rudani tun bayan da aka kashe shugabanta Mu'ammar Gaddafi A 2010 tare da taimakon kasashen turai wanda jirgin yakin Faransa ya yi sanadin raunata ayarinsa yayin da ya bar birnin Sirte akan hanyarsa ta neman mafaka lamarin da ya yi sanadi mutuwar dukannin masu tsaron lafiyarsa sakamakon haka kuma ya fada hannun 'yan tawaye wanda daga bisani suka kashe shi.

Tun bayan aukuwar lamarin ne bakaken fata 'yan Afrika suke fuskantar tsangwama da barazana iri-iri bayan Larabawa sun zarge su da taimaka wa marigayi shugaba Gaddafi a lokacin karshen mulkinsa.

CNN ce ta bankado badakalar cinikin bayi na karni na 19 inda ake azabtarwa tare da sayar da bakaken fata 'yan Afrika a matsayin bayi a kasar ta Libya.

**************************************** Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com **************************************** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN