Zargi: Yadda mazakutar matashi ya bace sakamakon yin musabaha

Wani hoton bidiyo da ke zagayawa a shafukan yanar gizo ya nuna cewa wani mutum ya rasa mazakutarsa bayan wani mutum ya gaisa da shi ta hanyar musabaha a garin Portharcourt ranar Asabar.

Lamarin ya faru a Emenike junction , matashi ya tsala ihu yayin da ya kula mazakutarsa ya bace bayan sun gaisa da wani matashi ta hanyar musabaha da hannu.

Ganin haka ne ya sa nan take ya biyo shi wanda suka yi musabahan ya rike shi lamarin da ya jawo hankalin 'yansanda na sashen SARS da ke wucewa cikin motarsu sai suka tsaya suka shiga tsakanin wanda ake zargi da sace mazakuta da wanda ke zargin mazakutarsa ta bace'

Bayanai sun nuna cewa mazakutar matashin ya dawo bayan da 'yansandan sun shiga tsakani.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Zargi: Yadda mazakutar matashi ya bace sakamakon yin musabaha Zargi: Yadda mazakutar matashi ya bace sakamakon yin musabaha Reviewed by on November 12, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.