November 22, 2017

Za a raba kan tagwaye da aka haifa kai manne da juna (Hotuna)

Likitoci a kasar Philippines suna gaf da fara wani aikin raba kan wasu tagwaye Joy da Joyce Magsino a aiki mai sarkakiya wadda ke iya kai wa ga mutuwar daya ko dukannin  tagwayen 'yan biyu mata masu shekara 10 da aka haifa kan su a manne da juna .

Iyayen yaran Patrick Magsino dan shekara 30 da matarsa Jomarie suna bukatar £75,000 kafin a yi wa tagwayen tiyatar.

Wasu hotuna sun bayyana inda aka ga tagwayen a wani Asibiti a gabacin Anjuan kusa da Manila ana yi masu gwaje gwaje da ke iya zama shirin mataki na farko domin yi masu aikin tiyata.


Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

0 comments:

Post a Comment

Rubuta ra ayin ka

Item Reviewed: Za a raba kan tagwaye da aka haifa kai manne da juna (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
Koma Sama