Yunkurin juyin mulki ? an ba Mugabe awa 24 ya sauka daga mulki (Hotuna)

Rahotanni daga kasar Zimbabwe sun nuna cewa aikwai jita-jita da ke zagayawa a kasar bayan an ga wasu tankokin yaki sun doshi babban birnin kasar Harare ranar Talata bayan wata zafafar muhawwara da ta taso tsakanin shugaba Robert Mugabe da Kwamandan dakarun kasar.

Bayanai sun nuna cewa an ba shugaba Mugabe awa 24 ya sauka daga mukaminsa sakamakon sallamar mataimakin shugaban kasar  da ya yi wanda tsohon Soja ne.

Wani ganau ya ce wasu tankokin yaki sun doshi babban birnin kasar da rana yayin da wasu guda biyu  aka girka su a Chinhoyi wacce take kilomita 14 zuwa Harare,haka zalika an ga dakaru sanye da damarar yaki girke tare da tankokin yakin.Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Yunkurin juyin mulki ? an ba Mugabe awa 24 ya sauka daga mulki (Hotuna) Yunkurin juyin mulki ? an ba Mugabe awa 24 ya sauka daga mulki (Hotuna) Reviewed by on November 15, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.