November 21, 2017

'Yan sanda sun kama mata da masu gadi 3 na gidan marigayi Bilyamin

Hukumar 'yansanda a birnin Abuja ta kama wasu masu gadi su uku da suke gadi a gidan Bilyamin Muhammed Bello 'da ga Dr. Bello Haliru wanda ake zargin matarsa Maryam Sanda ta kashe sakamakon kishi bayan ta ga wani sakon SMS a wayar salularsa.
Matar 'dan Dr. Bello Haliru ta kashe mijin ta Bilyamin sakamakon kishi
Mai magana da yawun hukumar 'yansanda na birnin Abuja ya ce an sami wani hoton bidiyo na CCTV inda aka ga masu gadin suna saka Bilyamin a cikin mota kafin a tafi da shi Asibiti.
Mubi: Tashin bom a masallaci ya kashe mutum 50 lokacin sallar asuba
Wata majiya ta labarta cewa Asibitoci guda biyu sun ki su karbi Bilyamin ganin irin halin da yake ciki kafin dagab bisani a ayyana rasuwarsa.
Kakakin 'yansanda na birnin tarayyan ya ce an kama Matar  Bilyamin watau Maryam dangane da zancen mutuwar mijinta Bilyamin. Ya ce rundunar tana tsare da Maryam tun ranar Lahadi.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

0 comments:

Post a Comment

Rubuta ra ayin ka

Item Reviewed: 'Yan sanda sun kama mata da masu gadi 3 na gidan marigayi Bilyamin Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
Koma Sama