Wa zai ba wani hanya,tawagar Gwamna ko na Minista ? jami'an tsaron su sun ja daga

Da safiyar Asabar tawagar motocin Gwamnan jihar Rivers  Nyesom Wike da na Ministan zirgazirga Chibuike Amarachi sun fuskanci juna gaf-da-gaf a daidai wata mahadar hanya a Nwanja da ke Trans Amandi sakamakon haka tawagar suka yi cas suna kallon juna domin kowane bangare ya ki ya jaye wa daya bangaren.

Hakan ya sa jami'an tsaron Gwamna da na Minista suka fito suna kalubalantar juna a wani yanayi da ya haifar da dar-dar a tsakanin jami'an tsaron ganin yadda kowane bangare ya hau kan bakansa akan cewa maigidansa ne ke da iko a jaye masa.

Daga bisani komai ya daidaita bayan manyan jami'an tsaro a cikin tawagar guda biyu sun fahimci juna wanda hakan ya sa motocin suka jaye wa juna kuma kowane ya wuce lafiya kalau.





Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN