Uba ya azabtar da 'dansa da dutsin guga mai zafi domin ya canye masa abinci

Hukumar da ke kare mutumci da fataucin yara ta kasa  watau National Agency for the Prohibition of Trafficking in Persons, NAPTIP ta kama wani mai aikin Pulomba mai suna Godstime Ategho 'dan shekara 29 bayan ya yi amfani da dutsin guga mai tsananin zafi ya daba a jikin 'dan sa mai shekara bakwai a Abuja.

Wani jami'in NAPTIP ya ce Ategho wanda 'dan asalin karamar hukumar Etiope ta gabas a jihar Delta ya daure yaron ne daga bisani ya saka dutsen guga da yayi zafi sai ya dinga gogawa a jikin yaron domin ya zargi yaron cewa ya canye mashi abinci da ya ajiye.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Uba ya azabtar da 'dansa da dutsin guga mai zafi domin ya canye masa abinci Uba ya azabtar da 'dansa da dutsin guga mai zafi domin ya canye masa abinci Reviewed by on November 21, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.